Indiyawa sun sayi Blackburn Rovers

Blackburn Rovers
Image caption Blackburn Rovers ce ta baya-bayan nan da aka sayar a Ingila

Iyalan Rao da suka fito daga kasar India sun kammala sayen kungiyar Blackburn Rovers ta Ingila a kan fan miliyan 43.

Gidauniyar da tsohon mai rike da kungiyar Jack Walker ya kafa ne suka sayar da kashi 99 da digo 9 na hannun jarin da suke da shi a kungiyar ga wani sabon kamfani Venky's London Limited.

Shugaban gidauniyar Paul Egerton-Vernon ya ce: "Mun gamsu da yadda muka mika ragamar Blackburn Rovers ga iyalan Rao."

"Mun amince da sha'awar da suka nuna ta zuba jari da kuma ciyar da kungiyar gaba, tare da kare manufofin Jack Walker."

Shi ma shugaban Venky Anuradha J Desai ya ce: "muna murna da samun damar yin harka a kungiyar Blackburn Rovers".