Lagerback zai koma Wales

Lars Lagerback
Image caption Lagerback ya ce ya tattauna da Hukumar Kwallon Kafa ta Wales

Tsohon kicin Najeriya da Sweden Lars Lagerback shi ne ake saran zai zamo sabon kociyan kungiyar kwallon kafa ta kasar Wales.

"A rubuce aiki ne mai ban sha'awa... Kana bukatar sanin yadda aikin zai kasance da kuma tsarin aikin," kamar yadda ya shaida wa Sport Wales.

Lagerback ya bi sahun Ian Rush da Lawrie Sanchez da Brian Flynn cikin wadanda ake saran za su gaji John Toshack.

Kociyan mai shekaru 62 dan kasar Sweden, ya ce ya tattauna da Hukumar Kwallon Kafa ta Wales a ranar 28 ga watan Satumba dama kuma wannan makon.