Rooney zai dawo fagen daga

Wayne Rooney
Image caption Rabon Rooney da taka leda tun ranar 16 ga watan Oktoba

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney, zai dawo taka leda daga raunin da ya ke fada da shi, a wasan da United za ta kara da Wigan a ranar Asabar.

Dan wasan mai shekaru 25, rabonsa da taka leda tun ranar 16 ga watan Oktoba, kuma kwanan nan ya dawo daga Amurka inda ya yi atisayi da kuma jinya.

"Ba na zaton za a fara wasan da shi," a cewar kociyan United Alex Ferguson. " Ba mamaki ya zauna a benci.

"Amma tabbas zai taka leda ranar Laraba a wasan da za mu kara da Rangers."

Duk da cewa bai dawo horo baki daya ba, Rooney ya yi atisayi sosai da zai ba shi damar fitowa a benci a wasan na ranar Asabar.

Dawowar Rooney za ta karfafawa Ferguson guiwa, wanda ke fama da rashin tabbacin Ryan Giggs da kuma Rafael.