Chelsea da Arsenal sun sha kashi a gasar Premier

Chelsea
Image caption Kociya Carlo Ancelotti yana cikin tsaka mai wuya

Chelsea wacce ke kan gaba a gasar Premier ta Ingila ta sha kashi a karo na biyu a jere, bayanda Birmingham ta doke ta da ci daya mai ban haushi.

A yanzu banbancin kwallaye ne ya raba Manchester United ta Chelsea, inda kowannen su ke da maki 28, bayanda United ta doke Wigan da ci 2-0. Lee Bowyer ne ya zira kwallo dayan da ta baiwa Birmingham nasara a filin wasa na St Andrews.

Wannan shi ne karo na uku da Chelsea ta sha kashi a wasanni hudu da ta buga a gasar Premier ta bana.

Ita ma Arsenal ta sha kashi a hannun Tottenham da ci biyu da uku a filin wasanta na Emirates.

Wannan ya sa Arsenal din ta koma mataki na uku daga na biyu, inda Manchester United ta shige gabanta.

Sakamakon wasannin Premier

Arsenal 2-3 Tottenham Man Utd 2-0 Wigan Bolton 5-1 Newcastle Blackpool 2-1 Wolves West Brom 0-3 Stoke Liverpool 3-0 West Ham