Ian Poulter ya lashe gasar Hong Kong Open

 Ian Poulter
Image caption Wannan ce nasara ta biyu da Ian Poulter ya samu a bana

Dan kasar Ingila Ian Poulter ya lashe gasa ta biyu a bana, bayanda ya samu nasara a gasar Hong Kong Open.

Poulter wanda dama shi ne ke jagoranci a gasar, ya tsallake kalubale daga wurin takwaransa na Ingila Simon Dyson wanda ya zo na biyu tare da Matteo Manassero.

Graeme McDowell na Ireland ta Arewa shi ne ya zo na biyar a gasar.

Jim kadan bayan nasarar da ya samu, Ian Poulter ya shaida wa BBC cewa:

"Mutane da dama ka iya kaiwa ga mataki na daya a duniya, kowa daga cikin 'yan wasa goma da ke sama na da damar matsawa gaba a jerin 'yan wasan da su ka fi kwarewa a fagen Golf".