Pillars ta sha kashi a hannun Kwara United

Bajon hukumar NPL
Image caption Wannan ne zagaye na uku na gasar ta Premier

Kano Pillars ta sha kashi a hannun Kwara United da ci daya mai ban haushi a gasar Premier ta Najeriya. A minti na 95 ne Isiaka Olawale ya zira kwallon.

Wannan wasa da a ka buga a filin wasa na garin Illori, babban birnin jihar Kwara, shi ne zagaye na uku a gasar ta bana.

Kungiyar Shooting Stars ta garin Badin ta doke Bukola Babes da ci 2-0, abin da ya ba ta damar darewa saman tebur da maki bakwai.

Gombe United ce ke biye mata baya da maki bakwai, bayanda ta doke Lobi Stars da ci daya da nema.

Wasu daga cikin sakamakon wasannin da a ka kara

Niger Tornadoes FC 0 - 0 JUTH FC Kwara United 1 - 0 Kano Pillars FC Shooting Stars 2 - 0 Bukola Babes Plateau United 0 - 1 Sunshine Stars FC Gombe United FC 1 - 0 Lobi Stars FC Sharks FC 1 - 0 Dolphin Port H…