Alan Shearer ya soki Fabio Capello

Alan Shearer
Image caption Alan Shearer ya dade yana takawa Ingila leda

Tsohon dan wasan Ingila Alan Shearer ya nuna shakku kan irin nasarorin da kasar ta samu karkashin jagorancin kociya Fabio Capello.

Kashin da Ingila ta sha a hannun Faransa a filin wasa na Wembley ranar Laraba, ya jefa damuwa a kasar kan makomar kungiyar ta Three Lion.

"Fabio ya shafe shekaru biyu da rabi a nan, amma ba ni da tabbas ko mun samu wani ci gaba na azo a gani," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Ko da a ce duka 'yan wasan Ingila na da lafiya, babu tabbas ko ya san irin dabarar da zai yi amfani da ita da kuma 'yan wasan da zai yi amfani da su."

Alan Shearer ya kuma nuna shakku kan kwarewar 'yan wasan Ingila idan a ka kwatanta su da takwarorinsu na waje.