Ancelotti ya ce yana nan daram a Chelsea

Image caption Carlo Ancelotti

Carlo Ancelotti ya ce ba ya fuskantar matsin lamba a matsayin kocin Chelsea, saboda haka zai ci gaba da zama a kungiyar har sai kwantaraginsa ya kare.

Ancelotti ya karyata rohatanni a Ingila da suke nuni da cewa zai bar kungiyar ta Chelsea, saboda wata takaddama da ta taso kan wa ke da ikon tafiyar da 'yan wasan kungiyar.

Ancelotti ya ce; "Rohatanni da aka yayata a wasu kafafen yada labarai cewa zan yi murabus ba su da tushe. Ban san abin da ya sa suka wallafa labaran ba, ina da kwantaragi da kungiyar har zuwa shekara ta 2012." A makon daya gabata ne dai Chelsea ta sallami mataimakin kocin kungiyar Ray Wilkins inda ta maye gurbinsa da Mike Emenalo wanda dan Najeriya ne. Ancelotti dai ya ce ba zai bari Emenalo ya hori kungiyar ba.