An cafke tsohon kocin Togo Tchanile Souradji Bana

Image caption Tawagar Togo na bogi

An kama tsohon kocin tawagar kwallon kafa ta Togo Tchanile Souradji Bana watanni biyu bayan an zarge shi da da amfani da sojojin gona a matsayin tawagar Togo, wajen buga wasan sada zumunci da Bahrain.

Tchanile Souradji Bana wanda da baya ake kyautata zaton ya tsere daga kasar, 'yan sanda sun cafke shi ne a wata mafaka a babban birnin Togo Lome.

An dai dakatar da Kocin na tsawon shekaru uku bayan wasan. Bahrain dai ta yi nasara ne akan Togo a wasan sada zumunci da ci uku da nema, amma dai Kocin Bahrain ya yi korafin cewa 'yan wasan basu da kwarewa, saboda wasan baiyi armashi ba.