David Cameron zai kai ziyarar kamun kafa Zurich

Image caption Pira Ministan Burtaniya, David Cameron

Pira Ministan Burtaniya David Cameron zai kai ziyarar kwanaki uku Zurich a mako mai zuwa, domin neman kamun kafa ga mambobin FIFA, a kokarin da Ingila ke yi na daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2018.

Pira Ministan ya dau matakin kai ziyarar ne kafin kwamitin zartarwa na hukumar FIFA ya kada kuri'ar amincewa da kasar da ta dace ta dauki bakuncin gasar wanda za a yi a ranar 2 ga watan Disamba.

Akwai yiwuwar Cameron zai gana da membobin kwamitin 22 a lokacin ziyarar ta sa.

Kasashen Russia da Spain/Portugal da kuma Netherlands/Belgium duk suna takarar neman daukar bakuncin gasar.

Ana dai kyautata zaton Cameron zai kai ziyarar birnin Zurich ne a Switzerland, kwanaki biyu, kafin FIFA ta kada kuri'a kan kasar da za ta dauki bakuncin gasar.