An dakatarda Samuel Eto'o a Italiya

Image caption Samuel Eto'o

An dakatar da dan wasan Inter Milan Samuel Eto'o daga wasanni uku a gasar Serie A, bayan ya yi wa dan wasan Chievo Bostjan Cesar karo a kirji.

Eto'o ya yi wa dan wasan karo ne a wasan da Cheivo ta doke Inter Milan da ci 2-1 a gasar serie A da a ka buga a karshen mako.

Alkalin wasa bai dau mataki a wasan ba, amma dai Hukumar kwallon Italiya ta dau matakin dakatar da dan wasan ne bayan ta kalli hotunan bidiyon wasan.

A kwanakin baya dai Hukumar kwallon Italiya ta yi amfani da hoton bidiyo wajen dakatar da dan wasan Fiorentina Alberto Gilardino, saboda ya zura kwallo da hannunsa.

Harwa yau dai Hukumar kwallon Italiya ta ci tarar Samuel Eto'o Fam 25,600, amma dai dan wasan zai samu buga wasa a gasar zakarun Turai