Federer ya lallasa Murray a gasar ATP a London

Image caption Roger Federer

Roger Federer ya lallasa Andy Murray a gasar Tennis ta ATP a London inda ya karbi ragamar jagoranci a rukunin B.

Roger Federer wanda shi ne na biyu a duniya a fagen Tennis ya doke Murray ne a wasanni biyu da suka buga da maki 6-4 6-2.

Federer dai ya doke Ferrer a gasar a ranar Lahadi kafin haduwarsa da Andy Murray.

A yanzu haka dai Federer na dab da tsallakewa zuwa zagayen wasan kusa da na karshe a gasar.