Samuel Eto'o ya nemi afuwa

Image caption Samuel Eto'o

Dan wasan Inter Milan Samuel Eto'o ya nemi afuwa, saboda karon da ya yi wa dan wasan Cheivo a ranar Lahadi a gasar Serie A.

Hukumar kwallon kafar Italiya dai ta dakatar da Eto'o na tsawon wasanni uku a gasar Serie A, saboda karon da ya yi.

"Ina neman afuwa ga duk wadanda abin da na yi ya shafa. Na yi nadama sosai. A gakiya ban san abin da ya sa nayi hakan ba." In ji Eto'o a wata sanarwa da ya fitar. "Har wa yau ina neman afuwa ga kungiya ta da mai horar da ni da kuma Shugaban Kungiyar Inter Milan Massimo Moratti, wanda a kullum ya ke bani kwarin gwiwa."