Mourinho ya karyata zargin neman jan kanti da gangan

Image caption Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya karyata zargin da ake yiwa 'yan wasan shi biyu cewar sun nemi a basu jan kati ne domin su samu bugawa a zagaye na gaba na gasar zakarun Turai.

Sergio Ramos da kuma Xabi Alonso sun samu katin gargadi na biyu ne bayan suna ba ta lokaci a wasan da Real Madrid ta doke Ajax da ci hudu da nema.

A yanzu haka dai, 'yan wasan biyu ba za su samu buga wasan karshe da kungiyar za ta kara a rukunin G ba.

Hukumar UEFA dai ta ce kwamitin da'ar ta ya duba al'amarin da niyyar daukar matakin da ya dace.