UEFA na tuhumar Mourinho da 'yan wasan Real Madrid 4

Image caption Jose Mourinho

Uefa na tuhumar Madrid bisa zargin rashin bin ka'adi da Kocin Kungiyar Jose Mourinho da kuma 'yan wasa hudu a kungiyar su ka nuna a gasar zakarun Turai.

Laifin da UEFA ke zargin Madrid da shi su shafi Mourinho da Xabi Alonso da Sergio Ramos da Iker Casillas da kuma Jerzy Dudek, a wasan da kungiyar ta doke Ajax da ci hudu da nema a gasar zakarun Turai da aka buga a ranar talata.

An dai nunawa Ramos da Alonso katin gargadi na biyu, bayan suna bata lokaci a wasan, abin da kuma ya sa 'yan wasan ba za su samu buga wasa na gaba ba a rukunin da suke.

An dai zargin 'yan wasanne da nema buga wasan zagayen kifa daya kwalla a gasar abin da kuma yasa suka nemi a basu katin da gangan.

Tini dai Mourinho ya karyata zargin da akayi game da 'yan wasanshi.