Alkalan wasa a Scotland za su shiga yajin aiki

Image caption Alkalan wasa

Kungiyar alkalan wasa a Scotland sun ki janye barazanar da suka yi na shiga yajin aiki a karshen mako, bayan sun kasa cimma matsaya da hukumar kwallon kasar.

Hukumar kwallon Scotcaland wato SFA, ta ce za ta nemi alkalan wasa daga wasu kasashe domin taimakawa da wasannin da za a buga a karshen mako.

Hukumar ta yi alkawarin daukar mataki a kan kungiyoyin da kuma 'yan wasa da ke cin mutuncin alkalan wasa da mataimakan su.

Wasu alkalan wasa a Kasashen Ireland da Wales da kuma Sweden, sun yi alkawarin taimakawa Hukumar wajen hura wasanni a karshen mako.

Kungiyar alkalan wasa a Scotland dai za su shiga yajin aikin ne saboda suna zargin manyan kungiyoyi a kasar da musguna musu.