Barcelona za ta yi galaba a kan Madrid- In ji Pira Minista

Image caption Pira Ministan Spain Jose Luis Rodriguez Zapatero

Pira Ministan Spain Jose Luis Rodriguez Zapatero ya yi hasashen cewa Barcelona za ta lallasa Real Madrid da ci 4-2 a wasan da kungiyoyi biyu za su buga a ranar litinin mai zuwa.

Pira Ministan wanda ya kasance yana goyon bayan kungiyar Barcelona shekara da shekaru ya ce ba zai samu kallon wasan ba saboda za shi wani taro Libya.

Zapatero ya kururunta Barcelona, inda ya ce duk Spaniya babu wata kungiya dake kayatarwa wajen taka leda kamar Barcelona.

Real Madrid dai ce ke jagoranci akan tebur a gasar Serie Laliga, kuma tana gaban Barcelona ne da maki guda.