Real Madrid ta ce binciken UEFA ya ba ta mamaki

Image caption Alkalin wasa ya nunawa Xavi Alonso kati

Kungiyar Real Madrid ta Spaniya ta musanta zargin da Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai, ta yi mata na cewa za ta bincika kocin kungiyar da kuma 'yan wasa hudu da rashin bin ka'aidar kwallon kafa.

Uefa za ta dauki hukunci a kan Real idan ta tabbatar da cewa Xabi Alonso da Sergio Ramos sun nemi a basu katin gargadi ne da gangan a wasan da kungiyar ta doke Ajax da ci hudu da nema a gasar zakarun Turai.

Sallaman na nufi, 'yan wasan biyu ba za su buga wasan karshe a rukuni a maimakon wasan kifa daya kwalla.

"Real Madrid na cikin mamaki da matakin da UEFA ta dauka." In ji wata sanarwa daga kungiyar.

Akwai yiwuwar UEFA za ta dakatar da 'yan wasan da kuma kocin kungiyar idan ta tabbatar da laifin.