Ina da kwarin gwiwa Arsenal za ta kai ga gaci- In ji Wenger

Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya yaba da kwarewar da 'yan wasansa su ka nuna a wasan da kungiyar ta doke Aston Villa da ci hudu da biyu a gasar Premier.

Arsenal din dai ta sha kashi a makon daya gabata a hannun Tottenham da ci uku da biyu, kuma Arsenal din ce ta fara zura kwallaye biyu a wasan, kafin a tafi hutun rabin lokaci.

"A gaskiya 'yan wasan sun taka rawar gani, musamman idan aka yi la'akari da abin da ya faru a makon daya gabata." In ji Wenger.

"Ina da kwarin gwiwa za mu iya lashe kofin Premier a bana."