Chelsea ta buga kunnen doki da Newcastle

Image caption 'Yan wasan Chelsea na murna bayan da Kalou ya fanshewa Kungiyar

Chelsea ta koma matakin na biyu a tebur a gasar Premier ta Ingila bayan ta buga kunnen doki da Newcastle United inda suka tashi daya da daya.

Andy Carroll ne ya fara zura kwallon farko a ragar Chelsea, ana minti biyar da fara wasan , sanan Solomon Kalou ya fanshewa Chelsea kafin a tafi hutu rabin lokaci.

A yanzu haka dai Chelsea na bayan Manchester United ne da maki biyu, bayan nasarar da United din ta yi a kan Blackburn da ci bakwai da guda.

Chelsea dai tayi nasara ne a wasa guda cikin biyar da ta buga a jere.