Ferguson ya jinjanawa Berbatov

Image caption Dimitar Berbatov

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya jinjinawa dan wasan shi Dimitar Berbatov bayan dan wasan ya zura kwallaye biyar a wasan da United ta lallasa Blackburn da ci bakwai da guda.

Berbatov ya zama dan wasa na hudu a tarihin gasar Premier da ya zura kwallaye biyar a wasa daya bayan Andy Cole da Alan Shearer da kuma Jermain Defoe.

"Berbatov ya taka rawar gani matuka," In ji Ferguson.

"Gaskiya zura kwallon da dan wasan ya yi da wuri ya taimaka mishi, domin ya buga wasanni goma bai zura kwallo, ko guda ba."

Berbatov ya zura kwallon farko ne ana minti biyu da fara wasan.