Manchester United za ta kara da Liverpool a gasar FA

Bebatov
Image caption A yanzu Manchester United ce ta daya a gasar Premier

Manchester United za ta kara da abokiyar hamayyar ta Liverpool a filin wasa na Old Trafford a zagaye na uku na gasar cin kofin FA.

Wannan shi ne karawa daya tilo da za a yi tsakanin kungiyoyin Premier kamar yadda jerin rabon kungiyoyin ya nuna.

Leeds za ta garzaya zuwa Arsenal, yayin da masu rike da kanbun Chelsea za su fafata da Ipswich, sai Stevenage da za ta kara da Newcastle.

Kungiyar Leicester da Sven-Goran Eriksson ke jagoranta za ta karbi bakuncin Manchester City.

Za a buga wasannin ne a karshen makonnin 8/9 na watan Janairun shekara ta 2011.