Ghana ta fito da sunayen koci 5 da za ta tantance

Image caption 'Yan wasan Ghana na murnar zura kwallo

Hukumar kwallon kafa a Ghana ta fito da jerin sunayen masu horrad da 'yan wasa biyar domin tantance su a kokarinsu na daukar wanda zai jagoranci tawagar, kasar.

Herbert Addo, shine kadai kocin cikin gida cikin sunayen da hukumar ta fitar, kuma shi zai jagoranci tawagar Ghana, wanda za su taka leda a gasar cin kofin 'yan wasan cikin gida.

Sauran sunayen da hukumar ta fitar, sun hada da tsohon dan wasan Faransa Marcel Desailly wanda kuma haifafen Ghana ne da Goran Stevanovic da Humberto Coelho da kuma Can Vanli. Hukumar dai ba ta ambaci ranar da za'a tantance su ba, amma ta bayyana cewa za ta nada sabo koci ne a tsakiyar watan Disamba.