Barca ba ta kunya ta mu ba- Mourinho

Image caption Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya karta cewa Barcelona ta kunya ta kungiyarsa bayan ta lallasa ta da ci biyar da nema.

Barca ta doke Madrid ne a wasan El Clasico na farko da Mourinho ya jagoranta.

"Kungiya daya ta taka rawar gani daya kuma ba ta yi ba." In ji Mourinho. "An doke mu, amma ba'a kunya ta mu ba."

"dole ne a doke mu a wasan saboda bamu taka rawar gani ba."

"Na shaida wa 'yan wasa na cewar ba'a gama kakar wasannin bana ba, akwai sauran lokaci, komai na iya faruwa a bana."

Ba'a dai taba doke wata kungiya da Mourinho ya jagoranta ba da sama da kwallaye uku.