Hukumar NFF ta gabatar da Samson Siasia

Image caption Samson Siasia

Hukumar kwalllon kafa ta Najeriya NFF, ta gabatar da sabon kocin Super Eagles Samson Siasia ga manema labarai a babban filin wasa da ke Abuja.

Hukumar ta dau Samson Siasia ne na tsawon shekaru hudu, inda ta ce ta za ta kara tsawon wa'adin kwantiragin, idan kocin ya yi tasiri.

Samson Siasia ya maye gurbin Lars Lagerback wanda ya ki sabunta kwantaragin sa da hukumar bayan an fitar da Najeriya a gasar cin kofin duniya da ta halarta a kasar Afrika ta kudu.

Najeriyar dai ba ta lashe wasa ko guda ba a gasar.

Shugaban Hukumar NFF, Alhaji Aminu Maigari, ya ce hukumar za ta ba sabon kocin duk goyon bayan da yake bukata domin ya fitar da kasar daga kangin da take ciki.

A wata hira da ya yi da manema labarai, sabon kocin Samson Siasia, ya yi alkawarin farantawa 'yan Najeriya rai ta hanyar inganta tawagar Super Eagles.

Ya ce zai kafa wani sansani na musamman, domin horon 'yan wasan cikin gida a kasar, wanda ya ce, yana da kwarin gwiwa kasar na da 'yan wasan cikin gida da za su iya habaka tawagar ta Super Eagles.

Samson Siasia dai ya nemi 'yan Najeriya da su ba shi dan lokaci domin aiwatar da ayyukan da za su inganta tawagar ta Super Eagles.