West Ham ta lallasa Man United da ci 4-0

West Ham ta lallasa Man United da ci 4-0
Image caption Wannan ne karo na farko da Manchester United ta sha kashi a bana

West Ham ta samu gurbi a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin Carling a karon farko cikin shekaru 20, bayanda ta doke Manchester United da ci 4-0.

Wasan wanda aka kara a filin wasa na Upton Park mai cike da kankara, shi ne karo na farko da aka doke United a kakar wasanni ta bana.

Tsohon dan wasan United Jonathan Spector ya taka rawar gani inda ya zira kwallaye biyu, wadanda su ne na farko da ya taba zirawa a Ingila.

Dan wasan Najeriya Victor Obinna Nsofor ya taka rawar gani shi ma, inda ya shirya duka kwallaye hudun da a ka zira.

Duk da cewa United ba ta yi amfani da kwararrun 'yan wasanta ba kamar yadda aka yi tsammani, amma a kwai 'yan wasa irinsu Ryan Giggs da Darren Fletcher da Javier Hernandez.

Ita ma dai Arsenal ta tsallake zuwa zagayen kusa da na karshe, bayanda ta doke Wigan da ci 2-0 a filin wasa na Emirates.