Rasha da Qatar za su karbi bakuncin gasar cin kofin duniya

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta baiwa Rasha damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya da za a shirya a shekara ta 2018.

Rasha dai za ta karbi bakunci gasar ne a karo na farko a tarihi

Kwamitin zartarwa na hukumar mai mambobi 22 ne su ka kada kuri'ar zaben kasar da ta dace ta dauki bakuncin gasar a birnin Zurich.

Sauran kasashen da su ka nuna kwadayin neman karban bakuncin sun hada da Ingila da hadin gwiwar Spain/Portugal da kuma Belguim/Holland.

Ingila dai ta sa ran, samun damar daukar bakuncin gasar, bayan manyan jakadun ta sun ziyarci birnin Zurich, wadanda su ka hada da Fira Ministan Kasar David Cameron da Yarima Williams da kuma tsohon kyaftin din tawagar kasar David Beckham.

An dai fidda Ingila ne a matakin farko wajen kada kuri'a.

Qatar 2022

Image caption Shugaban FIFA, a lokacin dayake bayyana Qatar

Har yau dai FIFA ta baiwa Qatar damar daukar bakunci gasar cin kofin duniya da za shirya a shekarar 2022 ga Qatar.

Qatar dai itama za ta zama kasa ta farko a gabas ta tsakiya da za ta fara daukar bakunci gasar cin kofin duniya

Sauran kasashen da su ka yi takara da Qatar din sun hada da Amurka da Koriya ta kudu da Austrailiya da kuma Japan.