Kankara ta hana wasu wasanni a Burtaniya

Kankara ta hana wasu wasanni a Burtaniya
Image caption Cikin wasannin da abin ya shafa har da na Manchester United da Blackpool

Tsananin sanyi da kankarar da ake fama da su a wasu sassan Burtaniya, sun sa an fasa wasu wasanni da dama da aka shirya yi a karshen mako.

Yankin Scotland abin ya fi shafa, inda aka dage wasannin Premier gaba daya.

A Ingila ma an dage wasan Premier tsakanin Manchester United da Blackpool, yayin da aka dage wasu wasannin na Championship saboda rashin kyawun yanayi.

Ana dai ci gaba da duba halin da filayen wasa ke ciki, inda a yanzu aka dakatar wasanni uku na gasar Premier ta zari-zuga.

Kungiyoyi na shawartar magoya bayansu da su gudanar da bincike kan ko za a yi wasa tukunna kafin su tafi kallo.