CAF:Gyan da Drogba da Eto'o na takara

Gyan
Image caption Gyan na son kwace kambum Afrika a wajen Drogba

Matashin dan kwallon Ghana wanda ke taka leda a Sunderland Asamoah Gyan na daga cikin 'yan kwallo biyar da hukumar kwallon kafa ta Afrika-Caf ta kebe don bada kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na bana.

Baya ga dan Black Stars din akwai 'yan kwallon Ivory Coast biyu dake Chelsea wato Didier Drogba da Salomon Kalou.

Dan Kamaru Samuel Eto'o wanda ke bugawa Inter Milan kwallo da dan Mali Seydou Keita ne suka cika jerin mutane biyar din.

Za a zabge mutane biyu daga jerin don su rage su uku a ranar 11 ga watan Disamba kafin ranar 20 ga wata a bayyana wanda ya samu kyautar a birnin Alkahira.

Alkalan wasa da kaptin na kasashe 53 zasu kada kuri'a don zaban wanda zai samu kyautar.

Dan Ghana Kwadwo Asamoah da dan Algeriya Ryad Boudebouz da Moussa Maazou na Jamhuriyar Nijer ne suka takarar neman kyautar matashin dan kwallon Afrika a bana.

A bara dai Drogba ne ya samu kyautar amma a bana Etoo ake ganin zai samu kyautar saboda ya lashe gasar zakarun Turai data serie A a Italiya tare da Inter Milan.