FUS Rabat ta Morocco ta lashe kofin Confederation

caf
Image caption Wannan ne karon farko da FUS Rabat ta lashe gasa a Afrika

Kungiyar FUS Rabat ta kasar Morocco ta lashe gasar kofin Confederation na Afrika bayan ta samu galaba akan CS Sfaxien ta Tunisia ta daci uku da biyu a bugu na biyu na wasan karshe.

A bugun farko a Morocco an tashi babu ci amma sai gashi a gida 'yan Tunisiyan suka sha kashi.

Abdelfatteh Boukhriss ne ya fara bude fagen a bangaren FUS kafin Hamdi Rouid ya farke sannan sai Kamel Zaiem yaci kwallo a yayinda Mohamed Zouidi yaci kwallaye biyun da suka baiwa kungiyar nasara.

'Yan kallo dubu talatin ne suka koma gida da takaici sakamakon kashin da kungiyaru ta sha.

Haka zalika daya kungiyar ta Tunisia Esperance itama an doke ta a watan daya gabata a wasan karshe na gasar zakarun Afrika daci shida da daya.

A halin yanzu dai TP Mazembe ta Congo zata kara da FUS Rabat ta Morocco a wasa kofin gwanin Afrika a watan Junairun badi.