Gwarzon 2010 :Iniesta da Xavi da Messi na takara

Barca
Image caption Iniesta da Xavi na son kwace kambum gwarzon dan kwallon duniya a wajen Messi

An kebe sunayen 'yan kwallon Barcelona uku Andres Iniesta da Xavi Hernandez da kuma Lionel Messi don bada kyautar gwarzon dan kwallon duniya na bana da Fifa za ta bayar.

Iniesta da Xavi sun taimakawa Spain ta lashe gasar cin kofin duniya a karon farko a tarihinta a yayinda Messi ya taimakawa Barcelona ta kara lashe gasar La Liga a bana.

Messi ne ya samu kyautar a bara inda aka bashi gwarzon dan kwallon Turai da jaridar kasar Faransa ke bayarwa sannan da kuma gwarzon dan kwallon duniya da Fifa ke bayarwar amma a karon farko a hade kyautuka biyu waje daya.

Har wa yau, kocin Inter Milan Jose Mourinho wanda ya lashe gasar zakarun Turai dana serie A da kuma na FA a bana yana takaran neman kyautar koci mafi bajinta tare da kocin Spain Vicente del Bosque dana Barcelona Pep Guardiola.

A ranar goma ga watan Junairu ne za a sanarda wadanda za a baiwa kyautar.