Newcastle ta kori Chris Hughton a matsayin koci

Hughton
Image caption Tsohon kocin Newcastle Chris Hughton

Newcastle United ta raba gari da kocin 'yan kwallonta Chris Hughton saboda tangal tangal din da kungiyar keyi a halin yanzu.

Newcastle ta sha kashi a wajen West Brom a ranar Asabar, bayan ta tashi kunen doki tsakaninta da Chelsea sannan kuma Bolton ta lallasa ta daci biyar da daya a makwannin da suka wuce.

Hughton ya jagoranci Newcastle ta koma gasar Premier a watan Mayu bayan ta nutse a kakar 2009-10.

A halin yanzu Newcastle ce ta goma sha daya akan tebur a yayinda ta samu nasara a wasanni biyar cikin fafatawa 16.

Sanarwa daga adreshin yanar gizon kungiyar ta ce "muna yiwa Chris godiya saboda rawar daya taka amma yanzu zamu maida hankali ne a wajen neman sabon koci".