London 2012: Magajin garin London ya yi amai ya lashe

Magajin garin London ya yi amai ya lashe
Image caption Ingila ta sha kashi a hannun Rasha bayanda ta samu kuri'u biyu

Magajin garin London Boris Johnson ya soke kyautar da ya yiwa jami'an FIFA na zama kyauta a babban hotel din Dorchester na London a lokacin gasar Olympics ta 2012.

Shi dai Magajin garin ya bayyana cewa zai baiwa Shugaban FIFA Sepp Blatter da tawagarsa damar zama kyauta a lokacin gasar ta Olympics.

Amma bayan matakin da FIFA ta dauka ranar Alhamis a zaben kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 inda Ingila ta samu kuri'u 2 a cikin 22 - sai ya sauya shawara.

Kasar Rasha dai aka zaba ta dauki bakuncin gasar.

Kwamitin shirya gasar ta Olympics ne dai ke da alhakin bada kyautar wurin zama ga manyan baki, kuma ana ganin Mr Johnson ya tattauna da kwamitin kafin ya dauki matakin.