Sai a badi Vermaelen zai koma takawa Arsenal kwallo

Vermaelen
Image caption Kusan watanni uku kenan Vermaelen yana jinya

Dan kwallon bayan Arsenal Thomas Vermaelen ba zai kara taka leda ba sai a badi saboda rauni a kafarshi.

Dan shekaru 24,Vermaelen ya jimu ne a wasan daya bugawa kasarshi Belgium na takarar neman gurbin a gasar kofin kasashen Turai na 2012 tsakaninta da Turkiya a ranar bakwai ga watan Satumba.

Kocin Gunners Arsene Wenger ya bayyana cewar a halin yanzu dan kwallon ya soma murmurewa tayin la'akari da hoton kafarshi da aka dauka.

Wenger ya siyo Vermaelen ne akan pan miliyan goma ne da kungiyar Ajax ta Holland a shekara ta 2009.

A halin yanzu dai Arsenal na fama da karancin 'yan kwallo inda Cesc Fabregas ke fama da ciwon kafada sannan kuma Abou Diaby ke fama da rauni a idon sawun shi.