Ana binciken jami'an hukumar kwallon Ghana a kan rashawa

Nyantakyi
Image caption Kwesi Nyantakyi yana takun saka da gwamnati

Harkokin gudanar da kwallon kafa a Ghana sun tsaya cik bayan da hukumar yaki da rashawa ta kasar ta garke kofofin shiga harabar hukumar GFA a ranar Talata.

Jami'an hukumar yaki da rashawa sun hana jami'an GFA shiga ko fitowa daga ofishin dake birnin Accra saboda suna binciken wasu takardu.

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa dai ta haramtawa gwamnati yin katsalanda a harkokin kwallon kafa, kuma a baya ta dakatar da wasu kasashen akan hakan.

A wani kan rufe ofishinsu na sa'o'i uku da hukumar yaki da rashawa tayi, jami'an GFA sun kira taron gaggawa da za suyi a ranar Laraba.

Kakakin GFA Randy Abbey ya bayyana cewar jami'an yaki da rashawar na binciken wasu takardu ne da suka shafi yarjejeniya tsakanin GFA da kamfanonin dake daukar nauyinta.