Liverpool ta lallasa Aston Villa da ci 3-0

Liverpool ta lallasa Aston Villa da ci 3-0
Image caption Ana ganin wannan nasara za ta kara wa Liverpool kwarin guiwa

Tsohon kocin Liverpool Gerard Houllier bai ji dadin karawar da ya yi da tsohuwar kungiyar ta sa ba, bayanda Liverpool ta doke Aston Villa da ci 3-0 a gasar Premier.

Ngog ne ya fara zira kwallon farko a minti na 14, sannan Babel ya zira ta biyu bayan mintina biyu kacal, kafin daga bisani Maxi Rodriguez ya zira ta uku.

Houllier ya samu kyakkyawar tarba daga magoya bayan Liverpool a karon farko da ya koma klob din wanda ya bari a shekara ta 2004.

Sai dai kociyan wanda ya lashe kofuna hudu a shekara shida ya ji jiki bayanda aka shiga filin wasa.

Liverpool ta samu nasara ne duk da cewa kyaftin din ta Steven Gerrard da Jamie Carragher da Fernando Torres ba su buga wasan ba.