Newcastle za ta nada sabon koci a karshen mako

Newcastle na kan neman koci na din-din-din domin ya maye gurbin Chris Hughton da ta sallama a karshen mako.

Kungiyar dai ta bayyana aniyar ta na nada sabon koci a karshen karshen mako.

Tsohon kocin Southampton Alan Pardew na daya daga cikin wadanda ake kyautata zaton sai samu mukamin, a yayinda shi kuma tsohon kocin Tottenham wanda ya yi murabus daga kungiyar Ajax a ranar litinin shi ma yana kwadayin mukamin.

Newcastle wanda ta sallami Hughton bayan ya jagoranci kungiyar ta dawo gasar Premier ta ce kocin ba shi da kwarewar da take bukata.

Tsohon dan wasan kungiyar Alan Shearer wanda ya taba jagorancin kungiyar ya ce baya marmarin dawowa kan mukamin.