Tottenham ta jagoranci rukunin A, a gasar UEFA

Image caption 'Yan wasan Tottenham suna murna

Kungiyar Tottenham ta Ingila ba za ta hadu da manyan kungiyoyi ba a wasan zagaye na biyu a gasar zakarun Turai, bayan ta jagoranci rukunin A.

Tottenham dai ta buga kunnen doki ne da FC Twente a wasan karshe da kungiyoyin biyu su ka buga, inda su ka tashi biyu da biyu.

Inter Milan wanda ke bukatar da zura kwallaye masu yawa domin ta jagoranci rukunin, ta sha kashi ne a hannun Weder Bremen da ci uku da nema.

Tottenham ta jagoranci rukunin ne da maki 11, inda Inter Milan wadda ita ma ta tsallake a rukunin ta gama da maki goma, duk da kashin da ta sha.