Arsenal ta tsallake zuwa zagaye na biyu

Arsenal ta tsallake zuwa zagaye na biyu
Image caption Robin van Persie da Walcott da Sami Nasri ne suka zira kwallaye ukun

Arsenal ta tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai bayanda ta doke Partizan Belgrade da ci 3-1 a filin wasa na Emirates.

Robin van Persie da Walcott da Sami Nasri ne suka zira kwallayen da suka baiwa Arsenal din nasara.

Wannan shi ne karo na 11 a jere da Arsenal ke halartar wannan mataki a gasar ta zakarun Turai.

Sai dai nasarar da Arsenal din ta samu ba ta bata damar kasancewa kan gaba a rukunin H ba.

Sakamakon sauran wasannin da aka buga

AC Milan 0-2 Ajax Bayern Munich 3-0 Basle CFR Cluj-Napoca 1-1 Roma Marseille 1-0 Chelsea MSK Zilina 1-2 Spartak Moscow Real Madrid 4-0 Auxerre Shakhtar Donetsk 2-0 Braga