Hukumar GFA ta dakatar da wasannin cikin gida

Kwesi Nyantakyi
Image caption Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana Kwesi Nyantakyi

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ghana GFA, ta dakatar da wasannin cikin gida bayanda 'yan sanda suka kai samame a ofishinta.

A ranar Talata ne jami'an hukumar yaki da masu aikata manyan laifuka ta Ghanar, SFO, suka hana ma'aikatan GFA shiga ofisoshin su, sannan suka yi awon gaba da na'urori masu kwakwalwa da dama.

Ita dai gwamnatin kasar na zargin jami'an Hukumar ta GFA ne da almubazzaranci da wasu kudade da kamfanin Globacom ya ba ta domin gudanar da gasar League ta kasar.

Bayan aukuwar lamarin, shugaban hukumar kwallon kafar Ghanar, Kwesi Nyantakyi, ya ce GFA ta ba masu binciken amsa a rubuce, dangane da wasu tambayoyin da suka yi mata.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta ce tana duba lamarin, kuma dokokinta sun hana 'yan siyasa yin katsalandan a harkokin gudanar da kwallon kafa.