Newcastle United ta nada Alan Pardew a matsayin koci

Pardew
Image caption kocin Newcastle Alan Pardew

Newcastle United ta nada Alan Pardew a matsayin kocin 'yan kwallonta a yarjejeniya ta shekaru biyar da rabi.

Pardew wanda kungiyar Southampton ta koreshi a watan Agusta ya maye gurbin Chris Hughton, wanda aka kora ranar Litinin.

"Nayi murna matuka akan wannan damar da aka bani a daya daga cikin manyan kungiyoyi a Ingila", in ji Pardew.

Pardew me shakaru arba'in da tara zai jagoranci Newcastle a wasan na farko a ranar Asabar tsakaninta da Liverpool.

Pardew a baya shine mai horadda 'yan kwallon Reading da West Ham da kuma Charlton .

Mahukunta a kungiyar Newcastle dai sun kori Hughton ne saboda a cewarsu suna bukatar kocin dake da kwarewa sosai.