Barca ta kulla yarjejeniya da Qatar Foundation

Image caption Messi zai zura kwallo a kungiyar Barca

Barcelona ta kulla yarjejeniya da Kungiyar Qatar Foundation domin sanya tambarin gidauniyar a rigar wasan kungiyar.

Barcelona ne dai ta kai wajen shekaru 111 ba ta karbar talla daga kungiyoyi da kamfanoni.

Kungiyar dai za ta samu fam miliyan 125 a tsawon shekaru shida a tsarin yarjejeniyar.

Barcelona dai ta biya Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, domin ta yi amfani da tambarin sa a kan rigar kungiyar na tsawon shekaru biyar.

Wannan Yarjejeniyar na nufin cewa, kungiyar za ta yi amfani da tambari biyu kenan a rigunan 'yan wasan kungiyar.

Barcelona za ta rika samun fam miliyan 25 a kowacce shekara karkashin yarjejeniyar wacce za ta kare a shekara ta 2016.