An rufe kada kuri'a a zaben gwarzon dan kwallon Afrika na BBC

A ranar Juma'a ne aka rufe kada kuri'a a zaben dan wasan da zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na BBC a bana.

'Yan wasan Ghana biyu, Asamoah Gyan da Andre 'Dede' Ayew na cikin jerin 'yan wasan da ke takarar lashe kyauter.

Sauran sun hada da dan wasan Kamaru Samuel Eto'o da Yaya Toure da kuma Didier Drogba wadanda duk 'yan kasar Ivory Coast ne.

Za'a bayyana wanda ya lashe kyautar a ranar Juma'a 17 ga watan Disamba a shirin wasannin Afrika na BBC, wato Fast Track.

Wannan kyauta ita kadai ce irin ta da masu sauraro ke zaben gwarzon na su.

Dan wasan Sunderland Gyan da kuma na Marseille Ayew sun taka wa Ghana leda a gasar cin kofin duniya inda kasar ta kai zagayen wasan kusa da na karshe a karo na farko a tarihin gasar.

Eto'o kuma ya taimaka wa kungiyar shi ta Inter Milan, inda ta lashe gasar zakarun Turai da gasar Serie A da kuma gasar Copa Italiya.

Shi ma dai Drogba ya taimaka wa kungiyar shi ta Chelsea, inda ta lashe gasar Premier ta Ingila da kuma kofin FA. Toure, kuma ya zama dan wasan da ya fi kowa albashi a Ingila bayan komawarsa kungiyar Manchester City daga Barcelona, inda a nan ma ya taka rawar gani.