Caf 2010: An zabge Salomon Kalou da Seydou Keita

caf
Image caption A ranar 20 ga watan Disamba za a sanarda gwarzon dan kwallon Afrika

Takarar neman kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na bana da hukumar Caf zata bayar ya koma tsakanin mutane uku wato Didier Drogba da Samuel Eto'o da kuma Asamoah Gyan.

Hakan bai bada mamaki ba ganin cewar an fidda sunayen Salomon Kalou na Ivory Coast da kuma Seydou Keita na Barcelona daga cikin masu takara.

A bara dai dan kwallon Chelsea kuma kaptin din Ivory Coast Didier Drogba ne ya samu kyautar,amma a bana wasu na ganin cewa Eto'o da Gyan sun fishi haskakawa.

Shi dai Eto'o ya taimakawa Inter Milan ta lashe gasar zakarun Turai dana Serie A da kuma Copa Italiya amma dai Kamaru karkashi jagorancinshi bata taka rawar gani ba a gasar cin kofin kasashen Afrika dana duniya.

Ana shi bangaren dai Gyan, wanda ya koma Sunderland daga Rennes kuma ya haskaka a Ghana inda kasar ta taka rawar gani a gasar cin kofin kasashen Afrika dana duniya.

Masu horadda 'yan kwallon kasashen Afrika ne zasu zabi gwarzon dan kwallon Afrika na bana a ranar 20 ga watan Disamba a birnin Alkahira.