Drogba ya bararwa da Chelsea penariti tsakaninta da Tottenham

Drogba
Image caption Drogba ya jikawa Chelsea gari

Didier Drogba ya barar da damar baiwa Chelsea nasara akan Tottenham bayan da golan Tottenham ya kabe bugun penaritin dan Ivory Coast din ana gabda tashi wasan.

Tun a minti na sha biyar ne Roman Pavlyuchenko ya ciwa Tottenham kwallonta na farko sannan bayan an dawo hutun rabin lokaci sai Drogba ya farkewa Chelsea.

Sakamakon karawar ya nuna cewar tun bayan da Chelsea ta kori Ray Wilkins a matsayin mataimakin mai horadda 'yan kwallonta bata kara samun galaba akan kowacce kungiya ba gasar premiership sannan kuma ta samu maki shida ne kacal cikin kawara bakwai data yi.

Sakamakon sauran fafatawa a gasar premier: *Aston Villa 2 - 1 West Bromwich *Everton 0 - 0 Wigan Athletic *Fulham 0 - 0 Sunderland *Stoke City 0 - 1 Blackpool *West Ham United 1 - 3 Manchester City *Newcastle United 3 - 1 Liverpool *Bolton Wanderers 2 - 1 Blackburn Rovers *Wolverhampton … 1 - 0 Birmingham City