Dan Najeriya Emenike ya tunanin bugawa Turkiya kwallo

Emenike
Image caption Dan Najeriya Emmanuel Emenike

Dan Najeriya Emmanuel Emenike ya ce bai yanke shawarar ko zai takawa Super Eagles ba ko kuma a'a.

Dan shekaru ashirin da uku wanda ke taka leda a kungiyar Karabukspor, a halin yanzu kasar Turkiya na zawarcinshi ya buga mata kwallo.

Emenike ya ce yana matsala da hukumar kwallon Najeriya NFF saboda a cewarshi sun yimashi kafar angulu a kokarin na barin Afrika ta Kudu zuwa Turkiya.

Amma akwai yiwuwar sabon kocin Super Eagles Samson Siasia na shirin ganawa da dan kwallon a mako mai zuwa.