Schweinsteiger ya sabunta yarjejeniyarshi a Bayern

Bastian Schweinsteiger
Image caption Schweinsteiger ya share 'Real Madrid ya kulle da Bayern'

Bastian Schweinsteiger ya sabunta yarjejeniyarshi da kungiyar Bayern München har zuwa shekara ta 2016.

Dan kwallon ya sanarda hakanne bayan nasarar da Bayern ta samu akan Fc St Pauli daci uku da nema a ranar Asabar.

Yace"na sabunta yarjejeniya ta zuwa shekara ta 2016".

Sai dai shugaban Bayern Uli Hoeness ya bayyana cewar a sabuwar yarjejeniyar za a baiwa Schweinsteiger Euro miliyan goma a kowane shekara.

Wannan yarjejeniyar tasa Bastian Schweinsteiger zai zama dan kwallo mafi tsada a Bayern fiye da Franck Ribery.

A baya rahotanni sun nuna cewar Real Madrid da Manchester United da Chelsea na zawarcinshi.