Manchester City ta cewa Carlos Tevez babu inda zashi

Tevez
Image caption Carlos Tevez ya nuna muradin barin City

Kungiyar Manchester City taki amincewa da bukatar dan Argentina Carlos Tevez na barin kungiyar.

Dan shekaru ashirin da shida,Tevez ya ce yana kewan gida tun zuwanshi Ingila shekaru hudu da suka wuce.

Sanarwa daga kungiyar ta ce "muna matukar bakin ciki da wannan yanayin,musamman hallayyar wakilin Carlos".

An dakatar da Tevez a wasan da City ta doke West Ham a ranar Asabar, inda a yanzu ta kamo Arsenal a maki.

Tevez yayi musayar kalamai da kocinsa Roberto Mancini a lokacin da aka cire shi ana gabda tashi a wasansu da Bolton ranar hudu ga watan Disamba.

Kungiyar ta ce ba zata sauya tsarinta ba sannan zata cigaba saka Tevez ya taka mata leda a lokacin data ke so.

A cewar City, Tevez da Wakilinshi Kia Joorabchian suna ta matsa lamba akan yin garan bawul bisa yarjejeniyar shekaru biyar dake tsakaninsu.