Manchester City ba zata iya lashe gasa ba sai da Tevez-Malouda

maluda
Image caption Malouda ya jinjinawa kwarewar Tevez

Dan kwallon Chelsea Florent Malouda ya ce da kamar wuya Manchester City ta iya lashe kofi ba tare da dan Argentina Carlos Tevez a cikin tawagar ba.

A cewarshi kungiyoyi na bukatar gogaggun 'yan kwallo don samun nasara, kamar yadda Drogba yake a Chelsea.

A ranar lahadi ne Tevez ya rubutawa mahukunta a City wasikar cewa yanason ya barsu saboda yana kewan gida.

Baya ga haka akwai alamun rashin jituwa tsakanin Tevez din da kocinsa Roberto Mancini abinda wasu ke ganin cewar shine abinda yasa dan kwallon ke kokarin barin Eastlands.

Tuni dai mahukunta a City suka bayyana cewar ba zasu bar Tevez ya tafi ba.