2018 da 2022: Beckenbauer ya soki Fifa

beck
Image caption Tsohon dan kwallon Jamus Franz Beckenbauer

Tsohon dan kwallon Jamus, Franz Beckenbauer ya soki tsarin da hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta bi wajen sanarda kasashen da zasu dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 da 2022.

Beckenbauer yace Fifa ta kunyatar da kasashe wajen fadin yawan kuri'un da suka samu a wajen zaben.

Beckenbauer na daga cikin wadanda suka kada kuri'a a matsayinshi na jami'i a kwamitin gudanarwar Fifa inda yace an wulakanta Ingila wacce ta samu kuri'u biyu da Australia me kuri'a guda.

A rubutunshi na jaridar Jamus mai suna 'bild', Beckenbauer yace ko sauran wakilan kwamitin Fifa da suka kada kuri'a basu san yadda sakamakon ya kaya ba.

Beckenbauer tsohon kaptin kuma kocin Jamus ne sannan a shekara mai zuwa zai sauka daga kujerarshi ta kwamitin Fifa.